Rahotanni: Za A Yi Desmond Tutu Tiyata Saboda Karuwar Rashin Lafiya
Iyalan daya daga cikin tsoffin masu fafutuka da kuma fada da wariyar launin fata a kasar Afirka ta Kudu Archbishop Desmond Tutu sun bayyana cewar a yau Laraba likitoci za su yi masa tiyata a ci gaba da maganin cutar da take damunsa wacce ta yi sanadiyyar kwanciyarsa a asibiti tun watan da ya gabata.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo iyalan Archbishop Desmond Tutun suna fadin hakan a jiya Talata sai dai ya ce ba su yi karin haske kan dangane da hakikanin cutar da ya ke fama da ita wacce za a masa tiyatar ba, amma dai sun ce ba ta da alaka cutar kansar mafitsara da aka yi masa aiki kanta tun shekaru 20 din da suka gabata.
Sanarwar da iyalan suka fitar ta kara da cewa Archbishop din dan shekaru 84 a duniya wanda kuma ya taba karbar kyautar Nobel ta zaman lafiya yana ci gaba da samun sauki a asibitin da yake kwance a birnin Cape Town na kasar Afirka ta kudun.
A shekarar da ta gabata ma dai an kwantar da Archbishop Desmond Tutun a wani asibitin inda aka yi masa wata karamar tiyatar saboda wani kumburi da ya fuskanta a jikinsa. Mr. Tutu dai ya kasance mai tsananin suka da kuma adawa da mulkin wariyar launin fata a kasar Afirka ta Kudu daga mimbarinsa na wa'azi a lokacin tsohuwar gwamnatin nuna wariyar launin fata ta Afirka ta Kudun.