Tarayyar Afirka Za Ta Shiga Tsakani Don Magance Rikcin Zaben Kasar Gabon
Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta sanar da cewa aniyarta na turawa da wata tawaga ta manyan jami'anta zuwa kasar Gabon don shiga tsakani da nufin kawo karshen rikicin siyasa da ya bullo kai a kasar bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar inda aka sanar da shugaban kasar Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo kakakin kungiyar Tarayyar Afirkan Jacob Enoh Eben yayin da yake ishara da rikicin da ke faruwa a kasar Gabon din yana cewa: Tabbas wannan lamari ne mai muhimmancin gaske don haka nan ba da jimawa ba kungiyar AU din za ta tura da wata tawaga zuwa kasar Gabon din don shiga tsakani.
Kakakin Tarayyar Afirkan ya kara da cewa shugaban kasar Chadi wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Tarayyar Afirkan shi ne zai jagoranci wannan tawaga ta shiga tsakani don tattaunawa da bangarorin da abin da ya shafa da nufin ganin an samo hanyar da za a magance rikicin.
Rikicin siyasan dai ya kunno kai ne bayan da hukumar zaben kasar ta Gabon ta sanar da shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar inda shi kuwa babban mai hamayya da shi a zaben Jean Ping yayi watsi da sakamaon yana mai cewa shi ne ya lashe zaben; lamarin da ya janyo barkewar rikici da ya zuwa yanzu alal akalla mutane 6 sun mutu kana wasu kimanin dubu guda kuma suna tsare.