MDD tayi marhabin da matakin da Jean Ping ya dauka
MDD ta yi marhabin da matakin da dan takarar shugabancin kasar da ya sha kayi a kasar Gabon ya dauka
Kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar China ya nakalto Abdullah Batily manzon musamman na MDD a cikiyar Afirka jiya Juma'a na cewa matakin da dan takarar shugabancin kasar da ya sha kayi a kasar Gabon Jean Ping ya dauka na garzayawa Kotun kundin tsarin milkin kasar abin a yaba ne, kuma wannan mataki ya yi daidai da kirar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa 'yan siyasar Kasar ta Congo da su warware matsalar ta hanyar doka.
Mista Abdullahi Batily ya kara da cewa Jean Ping ya nuna halin dattako kuma hakan da ya yi ya nuna shi shugaba ne na gari,saidai bayan ya shigar da karar, Mista Ping ya yi gargadin cewa matukar kotun ta ki amincewar da bukatar sa kasar za ta sake tsindima cikin wani sabon rikici.Mr. Ping na bukatar kotun da ta amince da bukartasa ta sake kidayan kuri’un da aka kada a cikin watan da ya gabata.
Kotun dai na da kwanaki 15 don yanke hukunci game da karar da Ping ya shigar mata