Babban Kotun Zambiya Ta Ki Amincewa Da Hana Rantsar Da Shugaban Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10873-babban_kotun_zambiya_ta_ki_amincewa_da_hana_rantsar_da_shugaban_kasar
Babbar kotun kasar Zambiya ta yi watsi da bukatar da babbar jam'iyyar adawa da ta kasar UPND ta gabatar na a hana rantsar da shugaban kasar Edgar Lungu a wa'adin mulki na gaba da ake sa ran yi a jibi Talata, saboda zargin cewa an tafka magudi a zaben shugaban kasar da aka gudanar.
(last modified 2018-08-22T06:58:54+00:00 )
Sep 11, 2016 01:25 UTC
  • Babban Kotun Zambiya Ta Ki Amincewa Da Hana Rantsar Da Shugaban Kasar

Babbar kotun kasar Zambiya ta yi watsi da bukatar da babbar jam'iyyar adawa da ta kasar UPND ta gabatar na a hana rantsar da shugaban kasar Edgar Lungu a wa'adin mulki na gaba da ake sa ran yi a jibi Talata, saboda zargin cewa an tafka magudi a zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Babban lauyan shugaba Lungun, Tutwa Ngulube ne ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters hakan inda ya ce kotun ta ki amincewa da hana rantsar da shugaba Lungu don kuwa ba ta da hurumin dakatar da hukuncin da kotun da ke sama da ita ta zartar.

A kwanakin baya ne dai shugban jam'iyyar adawa ta Opposition United Party for National Development (UPND), Hakainde Hichilema kuma dan takaran shugabancin kasar da ya sha kaye ya bukaci kotun da ta yi watsi da hukuncin kotun kundin tsarin mulki na kasar wacce ta yi da bukatarsa ta karin lokaci don samun damar kalubalantar sake zaben Mr. Lungu din a matsayin shugaban kasar Zambiyan, yana mai cewa an tafka magudi a zaben 11 ga watan Augustan da ta gabata da aka yi zargin da Mr. Lungun yayi watsi da shi.

Lauyan Mr. Hichilema, Keith Mweemba ya ce jam'iyyar  UPND za ta ci gaba da bin diddigin lamari a kotun koli ta kasar.

A jibi Talata ce ake sa ran za a rantsar da Edgar Lungu a matsayin sabon shugaban kasar wanda yake mulkin kasar tun bayan da tsohon shugaban kasar Micheal Sata ya mutu a shekara ta 2014.