Rahoton Majalisar Dinkin Duniya Kan Masifar Yunwa A Nahiyar Afrika
Sep 14, 2016 11:57 UTC
Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoton cewa: Akwai miliyoyin kananan yara da suke fama da masifar yunwa a kasashen nahiyar Afrika.
Ofishin kula da jin kan bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya a yau Laraba ya fitar da rahoton cewa: Kananan yara 'yan kasa da shekaru biyar a duniya fiye da miliyan shida ne suke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki a sassa daban daban da ke nahiyar Afrika sakamakon haka suna fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka.
Rahoton ya kuma mafi yawan kananan yaran da suke fama da matsalar rashin abinci mai gina jikin sun fito ne daga irin kasashen da suke fama da tashe-tashen hankula.
Tags