Gwamnatin Saliyo Za Ta Dawo Da Zartar Da Hukuncin Kisa A Kasar
Sakamakon karuwar laifuffuka da tashin hankali a kasar Saliyo, gwamnatin kasar ta sanar da cewa tana shirin sake dawo da hukuncin kisa a kasar wanda aka dakatar a baya.
Kamfanin dillancin labaran Xianhua ya jiyo ministan cikin gidan kasar Saliyon Paolo Conteh yana fadin cewa sakamakon ci gaba da karuwar laifuffuka da yanayin tashin hankali a kasar, nan ba da jimawa ba gwamnati za ta sake dawo da hukuncin kisa a kan wadanda aka same su da irin wadannan manyan laiffuffuka, don kuwa kasar tana bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ministan cikin gidan ya kara da cewa tuni ya ba wa jami'an gidajen yarin kasar da su fara gyaggyara kayayyakin da ake amfani da su wajen zartar da hukuncin kisa don akwai yiyuwar a fara zartar da shi.
Rahotanni dai sun ce tun a shekarar 1998 zuwa yanzu ba a sake zartar da hukuncin kisa a gidajen yarin kasar ba duk da cewa har ya zuwa yanzu dokar tana nan cikin kundin tsarin mulkin kasar.