Gwamnatin Tunusiya Ta Kara Tsawon Wa'adin Dokar Ta Baci A Kasar
Gwamnatin Tunusiya ta sanar da kara wa'adin dokar ta baci da ta kafa a kasar tun a watan Nuwamban shekara ta 2015 da ta gabata da nufin shawo kan matsalar tsaro.
Bayan gudanar da zaman tattaunawa da fira ministan Tunusiya da shugaban Majalisar Dokokin Kasar: Shugaban kasar Tunusiya Beji Qa'id Essebsi ya sanar da kara wa'adin dokar ta baci da aka kafa a kasar tun a watan Nuwamban shekarar da ta gabata ta 2015 zuwa tsawon wata guda, daga gobe Litinin 19 ga watan Satumban shekara ta 2016 da muke ciki.
Daga cikin jerin ayyukan da dokar ta bacin ta haramta sun hada da gudanar da tarzoma, zaman taruka da zasu kai ga bullar rikici sakamakon haka aka rufe wajajen gudanar da sharholiya irin wasannin gargajiya da gidajen sayar da giya da sauransu.
Tun a ranar 24 ga watan Nuwamban shekara ta 2015 ne shugaba Beji Qa'id Essebsi ya sanar da kafa dokar ta baci a kasar ta Tunusiya bayan harin ta'addancin da aka kai kan motar da ke dauke da jami'an tsaron fadar shugaban kasa da ya yi sanadiyyar mutuwar 12 daga cikinsu,kuma kungiayr ta'addanci ta Da'ish ta dauki alhakin kai harin.