Bon Ki Moon A Kasar A Bujumbura.
(last modified Mon, 22 Feb 2016 19:23:16 GMT )
Feb 22, 2016 19:23 UTC
  • Bon Ki Moon A Kasar A Bujumbura.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Fara Aiki A Kasar Burundi

Babban magatakarar Majalisar Dinkin Duniya Bon Ki Moon Ya Fara ziyarar aiki a kasar Burundi a yau litinin.

Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) ya ce; Ziyarar ta Bon Ki Moon ita ce irinta ta farko da babban magatakardar majalisar dinkin duniya ya kai zuwa kasar adaidai lokacin da ta ke fama da dambaruwar siyasa.

Ana sa ran cewa babban magatakardar majalisar dinkin duniyar zai gamsar da gwamnatin kasar ta bude tattaunawa da 'yan hamayya domin fitar da kasar daga halin da ta ke ciki.

Wata kafa ta majalisar dinkin duniyar ta ce ziyarar tana da matukar muhimmanci domin kuwa Bon Ki Moon zai yi iya kokarin kokarinsa domin ganin cewa shugaba Pieer Nkurunziza ya bude tattaunawa da 'yan hamayya.

Har iya yau, babban magatakardar ta Majalisar dinkin duniya zai yi magana da mahukuntan kasar akan take hakkin bil'adama, wanda ya kara kamari tun lokacin da da kasar ta fada cikin rikicin siyasa.