Gargadin Shugaban Kasar Mali Dangane Da Dawowar Kungiyar 'Yan ta'adda.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11479-gargadin_shugaban_kasar_mali_dangane_da_dawowar_kungiyar_'yan_ta'adda.
Shugaban kasar Mali Ya yi gargadi akan yiyuwar dawowar kungiyoyin 'yan ta'adda.
(last modified 2018-08-22T06:58:58+00:00 )
Sep 24, 2016 04:50 UTC
  • Gargadin Shugaban Kasar Mali Dangane Da Dawowar Kungiyar 'Yan ta'adda.

Shugaban kasar Mali Ya yi gargadi akan yiyuwar dawowar kungiyoyin 'yan ta'adda.

Kamfanin Dillancin labarun Faransa ya ambato shugaban na Mali Ibrahim Bubakar Keita yana cewa; Kungiyoyi masu wuce gona da iri da na 'yan ta'adda suna son sake farfadowa, domin kawo cikas akan shirin zaman lafiya a kasarsa.

Shugaba Keita wanda ya ke halartar taron babban zauren majalisar dinkin duniya a birnin New york, a jiya juma'a ya  yi ishara da ci gaban da aka samu na sulhun da aka cimmawa, sai dai duk da haka kungiyoyin da su ke damfare da alqa'ida na kokarin kawo cikas.

Bugu da kari, shugaban na Mali ya yi ishara da karuwar fasa kwaurin makamai da ta mutane da kwayoyi sannan kuma da fadace-fadace a tsakanin kungiyoyin da su ka rattaba hannu akan yarjejeniyar sulhun.