An kashe Sojojin Tchadi guda 4
Sojojin Tchadi guda 4 sun rasa rayukansu sanadiyar wani hari da ake kyautata zaton 'yan kungiyar boko haram ne suka kai shi
Kafar watsa labaran Afirka time ya nakalto Majiyar tsaron kasar daga birnin N'Djamena na cewa a marecen jiya Assabar da misalin karfe takwas na Dare wasu mahara da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko haram ne sun kai hari kan Sojojin kasar a shinken Djoroye dake kusa da iyakar kasar da Jumhoriyar Nijer, inda suka kashe Sojoji guda 4.
A matsayin mayar da martani, Sojojin na tchadi sun hallaka maharan guda 7.
Tun daga shekarar 2009 ne kungiyar ta boko haram ta fara kai hare-haren ta a Najeriya, a shekarar 2015 kungiyar ta fadada kai hare-haren ta zuwa kasashen Nijer, Kamaru da Tchadi.kasashen Najeriya, kamaru, tchadi ,Nijer da Benin sun kafa wata Rundunar hadin gwiwa domin yaki da kungiyar Boko haram a yankin tabkin Tchadi.