ICC : An Yankewa Ahmad Al' Mahdi Hukuncin Daurin Shekaru 9
Sep 27, 2016 07:29 UTC
Kotun hukunta mayan laifuka ta Duniya wawo ICC ta yankewa dan jihadin nan dan asalin kasar Mali, wato Ahmad Al Faqi Al Mahdi hukuncin shekaru 9 a gidan yari bisa laifin lalata wuraren tarihi a kasar.
An dai tuhimi Ahmad Al Faqi Al Mahdi dai laifin lalata gidan tarihin Tubuctu na Mali dake karkashin kulawar hukumar kare wurare masu tarihi na MDD wato UNESCO.
Ahmad Al Faqi Al Mahdi dai ana tuhumarsa da hannu a laifuka da dama da kuma kasancewarsa kakakin kungiyar mayakan dake ikirarin jihadi a arewacin kasar Mali, kamar yadda daya daga cikin alkalan kotun ta ICC / CPI, Raul Pangalangan ya shaidawa kanfanin dilanacin labarai na Faransa AFP.
Tags