Jam'iyyar APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Edo A Nijeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11734-jam'iyyar_apc_ta_lashe_zaben_gwamnan_jihar_edo_a_nijeriya
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC) ta sanar da dan takarar jam'iyyar APC mai mulkin kasar, Godwin Obaseki, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Edo da ke yankin Kudu Maso Kudu na kasar da aka gudanar a jiya Laraba.
(last modified 2018-08-22T06:59:00+00:00 )
Sep 29, 2016 14:34 UTC
  • Jam'iyyar APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Edo A Nijeriya

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC) ta sanar da dan takarar jam'iyyar APC mai mulkin kasar, Godwin Obaseki, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Edo da ke yankin Kudu Maso Kudu na kasar da aka gudanar a jiya Laraba.

A cikin wata sanarwa da shugaban hukumar zaben jihar ta Edo Professor Kayode Soremekun ya sanar ya ce dan takarar jam'iyyar APC din Godwin Obaseki shi ne ya lashe zaben da kuri'u 319,483, sannan shi kuma babban dan hamayyarsa dan takarar jam'iyyar PDP Osagie Ize-Iyamu, ya samu kuri'u  253,173. 

Sanarwar hukumar zaben ta kara da cewa Mr. Obaseki na jam'iiyar APC din har ila yau ya lashe kananan hukumomi 13 daga cikin 18 na jihar, don haka sai shugaban hukumar zaben ya sanar da Mr. Obaseki a matsayin gwamnan da al'ummar jihar Edo din suka zaba.

To sai dai jam'iyyar PDP wacce ta sha kaye a zaben, ta bakin shugaban jam'iyyar ta jihar Edon Dan Orbih  ta ki amincewa da sakamakon zaben tana  mai cewa sakamakon da aka sanar a rumfunan kada kuri'un da kuma mazabu sun saba wa wanda hukumar zaben ta sanar. Jam'iyyar ta kara da cewa bisa ga wadancan sakamakon jam'iyyar PDP din za ta samu rinjaye na sama da kuri'u 30,000.

Kafin nan wasu rahotannin sun ce magoya bayan jam'iyyar PDP din sun zagaye ofishin hukumar zaben don nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben suna masu zargin kokarin tafka magudi.

Rahotanni daga jihar suna cewa magoya bayan jam'iyyar  APC din suna ta bukukuwan wannan nasara da jam'iyyar ta su wacce da man ita ce mai mulki a jihar  ta  samu.