Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnatin Mali A Birnin Bamako.
Oct 02, 2016 03:10 UTC
Dubban Mutane Sun yi Zanga-zangar kin jinin gwamnati A Bamako.
Kamfanin Dillancin Labarun Fransa ya ambato cewa; A jiya asabar mutane sun yi Zanga-zanga a titunan birnin Bamako domin nuna kin amincewarsu da sabuwar dokar zabe.
Mazu Zanga-zangar sun hada da fitattun 'yan siyasa da su ka hada tsohon pira minista Modibo Sidibe.
A ranar 9 ga watan Satumba ne dai,majalisar dokokin kasar ta Mali ta yi sabuwar dokar wacce ta kunshi cewa duk wanda ya ke son tsayawa takarar shugaban kasa, to dole ya biya kudin da su ka kai dalar Amurka 43,000.
"Yan hamayyar sun zargi kafafen watsa labarun kasar da kin bada labarin musabbabin yin zanga-zangar.
Tags