An karfafa matakan tsaro a kasar Uganda
(last modified Sun, 09 Oct 2016 17:46:15 GMT )
Oct 09, 2016 17:46 UTC
  • An karfafa matakan tsaro a kasar Uganda

A yayin kame shugaban 'yan adawa, jami'an 'yan sanda sun karfafa matakan tsaro a yankuna daban daban na birnin Kampala fadar milkin kasar Uganda

Kafar watsa labaran Afirka News ya habarta cewa bayan kame Kizza Besigye shugaban 'yan adawa na kasar Uganda yan sanda sun karfafa matakan tsaro a yankuna daban daban na birnin Kampala.

Rahoton ya ce jami'an tsaron sun kame shugaban 'yan adawar ne a yayin fitar sa daga cikin gidansa ba tare da wani karin haske ba kan musababin da ya sanya suka kame shi.bisa hukunci kotu,Mista Besigye har zuwa karshe shari'ar da yake fuskanta a gaban kotu wajibi ne ya nisanci duk wani rikici ko taro na siyasa a kasar.

Idan ba a manta ba, Mista Besigye Shugaban 'yan adawar da ya sha kayi ne a zaben da ya gabata  ya shelanta kansa a matsayin halarceccen shugaban kasar ta Uganda yayin da ake rantsar da Shugaba Yoweri Museveni, lamarin da ya sanya Gwamnati ta tuhume shi da laifin cin amanar kasa.wasu rahotanni sun ce , jami'an 'yan sanda suna zarkin Besigye ne da laifin tayar da tarzoma a birnin Kampala.

A bangare guda, Jam'iyun Adawa masu fafutukar tabbatar da tafarkin Demokaradiya a kasar sun bukaci a sake kirga kuri'u da aka kada a bayyane.

Rikicin Siyasa ya kara kamari tsakanin Gwamnati da 'yan adawa tun bayan zabe a kasar Uganda.