Shugabar Gwamnatin Jamus ta fara ziyara a kasashen Afirka
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Markel ta fara ziyara a kasar Mali
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa Shugabar Gwamnatin Jamus ta fara ziyarar kwanaki uku a yankin Afirka, inda a wannan Lahadi ta fara da kasar Mali, manufar wannan ziyara shi ne tattauna da Sojojin kasar dake aikin wanzar da zaman lafiya a wasu kasashen Afirka da kuma tattauna da shugabanin wasu kasashen domin zartar da kudirin hana kwararen bakin haure zuwa kasashen Turai.
Har ila yau Shugabar Gwamnatin ta Jamus za ta halarci taron bude ginin Kungiyar Tarayyar Afirka da Jamus ta dauki nauyin ginawa a birnin Addis Abeba fadar milkin kasar Habasha, za kuma ta gana da sojojin Jamus a Mali da Nijar wadanda ke zama wani bangare na dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali. Har ila yau a wannan ziyara shugabar gwamnatin za ta gana da shugabanni na kungiyoyin fafutika da masu tallafa wa 'yan gudun hijira .
A shekarar 2015 dai Jamus ta karbi bakuncin 'yan gudun hijira sama da dubu dari takwas mafi yawa daga Siriya da Afghanistan da wadanda ke gujewa talauci musamman daga kasashen Arewacin Afirka.