An sanar da dokar ta bace a yankin Tunbuktu na kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12349-an_sanar_da_dokar_ta_bace_a_yankin_tunbuktu_na_kasar_mali
Gwamnatin Kasar Mali ta shelanta dokar ta bace a garin Tunbuktu dake arewacin kasar
(last modified 2018-08-22T06:59:04+00:00 )
Oct 12, 2016 06:48 UTC
  • An sanar da dokar ta bace a yankin Tunbuktu na kasar Mali

Gwamnatin Kasar Mali ta shelanta dokar ta bace a garin Tunbuktu dake arewacin kasar

A cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Laraba, Gwamnatin Mali ta ce ta dauki wannan mataki ne domin kare lafiyar fararen hula da Dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin, wannan mataki na zuwa ne bayan wani yunkurin kai hari da wani dan kunar bakin wake ya yi a kusa da motar Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin da ta gabata.

Majiyoyin Gwamnatin ta Mali sun tabbatar da cewa bayan bindige maharin da Dakarun Majalisar dinkin Duniya suka yi, a kwai mahara biyu dake tare da shi sun gudu, kuma har yanzu ba a kai ga kame su ba.

Tun daga watan Maris na shekarar 2012 ne, masu da'awar kishin islama a yankin Magrib suka mamaye yankunan arewacin Mali, saidai bayan shigar Sojojin Faransa da na kasashen Afirka , an  fatattake su daga yankin.