An Gudanar Da Tarukan Ashura A Birnin Johannesburg Na Afirka Ta Kudu
An gudanar da gagarumin taron juyayin Ashura a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, tare da halartar bangarori daban-daban na musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa, taron Ashura da aka gudanar a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu ya gudana lami lafiya, inda jami'an tsaro suka dauki matakan bayar da kariya ga masu gudanar da tarukan.
An gudanar da irin wadannan taruka a kasashen duniya daban-daban, da suka hada da na gabas ta tsakiya, wasu kasashen Asia, da na turai da latin Amurka gami da wasu kasashen Afirka, inda aka yi tarukan aka gama lami lafiya, in banda a Afghanistan, inda 'yan ta'addan takfiriyya suka kai harin bam tare da kashe mutane 15, sai kuma Najeriya inda sojojin gwamnati tare da 'yan sanda suka afka wa tarukan na Ashura a wasu biranan kasar, musamman a Kaduna, Funtua da kuma Jos.