Jikkata Sojojin Faransa A Kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12421-jikkata_sojojin_faransa_a_kasar_mali
Jikkata Sojojin Faransa A Kasar Mali
(last modified 2018-08-22T11:29:05+00:00 )
Oct 14, 2016 05:37 UTC
  • Jikkata Sojojin Faransa A Kasar Mali

Jikkata Sojojin Faransa A Kasar Mali

Sojojin Faransa shida sun jikkata sanadiyyar fashewar wata nakiya a arewacin kasar Mali.

Kakakin sojan Faransa a kasar Mali,  Patric Stinger ya fada a jiya alhamis cewa;  Nakiyar ta tarwatse ne a yankin Abibara da ke arewacin kasar wanda ya yi sanadin jikkatar sojoji shida.

A gefe daya, majiyar sojan Mali ta ce; sojojinta biyu sun mutu, a lokacin da motar da ta ke dauke da su ta ci karo da nakiya.

A makon da ya shude ma, an sanar da mutuwar tsohon shugaban kungiyar 'yan tawayen buzaye na kasar Mali, sanadiyyar tashin wani bom.

A shekarar 2015 ne aka yi sulhu a tsakanin gwamnatin kasar mali da 'yan tawayen buzaye, bisa shiga tsakanin majalisar dinkin duniya.