'Yan Adawa A Kongo Sun Fara Nuna Adawarsu Ga Daga Lokacin Zabe
Rahotanni daga kasar Demokradiyyar Kongo sun bayyana cewar 'yan adawar kasar sun fara daukar matakin yajin aiki da zaman dirshan a duk fadin kasar don nuna rashin amincewarsu da dage lokacin zaben shugaban kasar da aka yi suna masu cewa hakan wani kokari ne na shugaba Joseph Kabila na ci gaba da mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran France Press daga birnin Kinsasha, babban birnin kasar Demokradiyyar Kongon ya bayyana cewar fara yajin aiki da zaman dirshan din ya biyo bayan nuna rashin amincewa da kuma bukatar da babban jami'ar adawa ta kasar ta yi ne ga al'ummar kasar da su nuna rashin amincewarsu da shirin jinkirta lokacin zaben shugaban kasar har sai zuwa watan Aprilun 2018.
Babbar jam'iyyar adawar ta UDA ta bayyana yarjejeniyar da gwamnatin kasar ta cimma da wasu 'yan kananan jam'iyyun kasar na dage lokacin zaben da cewa ya saba wa dokokin kasar, don haka suke ce za su ci gaba da nuna adawa da rashin amincewarsu da hakan.
Rahotannin sun ce an baza jami'an tsaro a yankuna na kasar musamman a babban birnin kasar don kare abkuwar karya doka da oda.
'Yan adawan dai suna zargin shugaba Joseph Kabila da kokarin ci gaba da mulkin kasar da hanyar kin gudanar da zaben shugaban kasa da ya kamata a gudanar a wannan shekarar.