Masar Na Kokarin Shiga Tsakanin Syria Da Majalisar Dinkin Duniya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12700-masar_na_kokarin_shiga_tsakanin_syria_da_majalisar_dinkin_duniya
Syria ta amince da shiga tsakanin da Masar din ta ke yi.
(last modified 2018-08-22T06:59:06+00:00 )
Oct 20, 2016 08:29 UTC
  • Masar Na Kokarin Shiga Tsakanin Syria Da Majalisar Dinkin Duniya

Syria ta amince da shiga tsakanin da Masar din ta ke yi.

Majiyar Diplomasiyyar Masar ta ce; Kasar tana kokarin samar da kafa ta aiki tare a tsakanin Syria da Majalisar Dinkin Duniya akan yankin Allepo.

Kamfanin Dillancin Labarun "Isna' na Iran ya ambato majiyar diplomasiyyar kasar Masar a yau alhamis na cewa; Jami'an diplomasiyyar kasar a birnin Damasscuss suna tattaunawa da jami'an gwamnatin Syria da kuma na Majalisar dinkin duniya domin ganin yadda za su yi aiki tare.

Majiyar ta kuma ce tuni gwamnatin Syria ta amince da shiga tsakanin da Masar din ta ke yi.