An kashe wani dalibin Jami'a a kasar Afirka ta kudu.
Bayan kwashe makuni na zanga-zangar Daliban jami'a a kasar Afirka ta kudu, fadar shugaban kasar ta sanar da kashe daya daga cikin daliban a kasar
Kamfanin dillancin labaran Reuters daga Johannesburg ya nakalto fadar Shugaban kasar Afirka ta kudu a wannan juma'a na cewa Dalibin Jami'an ya rasa ransa ne sanadiyar hadarin Mota a jiya Alkhamis a Pretoria birnin Siyasar kasar.
Rahotanni sun ce Jami'an 'yan sanda sun yi amfani da hayaki masu sanya hawaye wajen tarwatsa dariruwan daliban jami'a da suka tsuntsurundu a gaban Ofishin Shugaban Kasar Jacob Zuma a birnin Pretoria domin nuna adawarsu kan karin gudin karatu da magabatan jami'ar suke yi a ko wata shekara , tare da neman Gwamnati ta mayar da karatun kyauta a jami'o'in kasar gaba daya.
Bayan mutuwar Dalibin, labari ya watsu a cikin kasar kan cewa Jami'an 'yan sanda sun hallaka daya daga cikin shugabanin daliban Jami'a, lamarin da ya sanya fadar Shugaban kasar ta fito ta kara wata jita-jita tare da bayyana sanadiyar mutuwar ta sa.