Taro Kan Mahangar Kur'ani Kan Hadin Kan Musulmi A Senegal
Za a gudanar da wani zaman taro Ta'is na kasar Senegal kan mahangar kur'ani mai tsarki dangane da wajabcin hadin kan al'ummar musulmi.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya bayar da rahoton cewa, shugaban karamin ofishin jakadancin kasar Iran a Senegal Sayyid Hassan Ismati ne tare da shugaban darikar Ashabul yamin sheikh Muhammad Idris ne suka dauki nauyin shirya wannan taro a garin na Tais.
Taron wanda za a gudanar a cikin mako mai kamawa, zai samu halartar masana da kuma malamai daga sassa na kasar, kamar yadda zai samu halaratr wasu daga cikin masana na kasar Iran, wadanda za su bayyana mahangarsu dangane da kiran da Imam Khomein (RA) ya yi na wajabcin hada kai tsakanin musulmi, domin tunkarar abubuwan da suke a matsayin kalubale a gare su.
A nasa bangaren babban shehin darikar Muridiyyah wanda ya rubuta littafin tafsirin kur'ani mafi girma a Senegal Sheikh Ahmad Bamba ya sanar da cewa zai samu halartar taron.