Taron Koli Kan Mahangar Musulunci A Siyasar Duniyar Yau A Senegal
(last modified Tue, 25 Oct 2016 12:40:40 GMT )
Oct 25, 2016 12:40 UTC
  • Taron Koli Kan Mahangar Musulunci A Siyasar Duniyar Yau A Senegal

Ana shirin fara gudanar da wani taro na kasa da kasa a Senegal kan matsayin musulmi dangane da lamurra da suka shafi duniya yau.

Shafin yada labarai na Dakar.icro ya habarta cewa, taron zai yi dubi kan matsayin musulunci da mahangarsa kan lamurra da suka shafi dniya a yau wanda kasashen Iran da Senegal suka dauki nauyin shiryawa.

Taron dai wanda shi ne irinsa na farko, zai samu halartar masana daga kasashe 10, wadanda za su gabar laccoci tare da bayyana mahangarsu kan yadda ya kamata musulmi su fusknaci lamrran da suke wakana a duniya a halin yanzu.

Sheikh Bashir Mbaki babban daraktan cibiyar gudanar da tarukan addini na kasa da kasa a Senegal shi ne mai masafkin baki, inda sheikh Akhtari shugaban cibiyar Ahlul bait ta duniya yake a matsayin babban bako.