An Hallaka 'yan ta'adda da Dama A Jihar Hums na Kasar Siriya
Dakarun Tsaron Siriya Sun Hallaka 'Yan Ta'adda Da Dama A Jihar Hums
Tashar Telbijin din Al'alam wacce ke watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta nakalto majiyar tsaro Siriya na cewa, A jiya Assabar Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda da dama a wani gumurzu mai tsananin tsakanin su da 'yan ta'addar a yankin yammacin garin Talbisah dake arewacin garin Hums tare kuma da jikkata wani adadi mai yawa daga cikinsu, bayan asara mai dunbun yawa da suka yiwa 'yan ta'addar.
A nasu waje, Jiragen Yakin kasar Rasha sun kai hare-hare kan guraren taruwar 'yan ta'addar ISIS a kauyen Alhawaika na yankin Hisan, Gonakin Mari'iya da Hawijah Sakar dake gefen Dairi zur, lamarin da yayi sanadiyar hallaka da dama daga cikinsu tare kuma da jikkata wani adadi mai yawa na daban.
Har ila yau jiragen yakin na Rasha sun yi lugudar wuta a maboyar 'yan ta'addar dake gefen Lazikiya, yayin da su kuma Sojojin Siriya suka kai wani sumame a sansanin 'yan t'adda na tsaunukan kurdawa, inda suka hallaka 'yan ta'addar da dama.
a bangare guda kuma, ‘Yan adawar na Syria sun amince da su halarci zaman sasanta rikicin kasar da majalisar dinkin duniya ke jagoranta a birnin Geneva na kasar Switzerland, inda a baya suka yi barazanar kauracewa.