An kama 'yan jarida da dama a kasar Masar
A yayin da zanga-zangar kin jinin Gwamnati ta 11 ga watan Nuwamba ke kusantowa, kotun Masar ta bada izinin kama 'yan jarida 63 a kasar
Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya habarta cewa Kotun kasar Masar ta bada umarnin kame 'yan jarida 63 kan zarkin su da watsa labaran karya da kuma ingiza Al'umma na kawar da Gwamnatin kasar., har ila yau Kotun ta baiwa Jami'an tsaro izinin kai farmaki tare da bincike kan wuraren da ake buka jaridu na kungiyar 'yan uwa musulmi.
A cikin 'yan kwanakin da suka gabata ne wasu kungiyoyin fararen hula da na siyasa suka bukaci da gudanar da gagarumar zanga-zanga mai taken juyin milkin yunwa a ranar 11 ga watan Nuwamba mai kamawa.
Rahotanni sun ce daga farkon wannan wata da muke cikin 'yan jarida 4 ne jami'an tsaron Masar din suka kama a kusa da cibiyar 'yan jaridun dake tsakiyar birnin Alkahira, lamarin da ya janyo nuna fishi ga kungiyar 'yan jaridun kasar musaman ma bayan da ta samu labarin cewa mutanan na fuskantar bakar azaba daga Jami'an tsaro.
Daga farkon wannan shekara zuwa yanzu yawan 'yan jaridun da aka kama a kasar Masar ya haura zuwa 23, idan kuma aka kiyasta adadin da wadanda aka kama a shekarar 2014, adadin ya haura zuwa ninki biyu.