Jami'an Tsaron Aljeriya Sun Tsaurara Matakan Tsaro A Yankin Gabashin Kasar
Oct 31, 2016 07:37 UTC
Majiyar tsaron Aljeriya ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi dirar mikiya a yankin gabashin kasar ta Aljeriya da nufin zakulo wasu gungun 'yan ta'adda da suka kashe jami'in tsaron kasar.
Majiyar tsaron Aljeriya a yau Litinin ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi dirar mikiya a garin Qasnadinah a yankin gabashin kasar da nufin zakulo wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish da ake kyautata zaton suna da maboya a yankin.
A ranar Juma'a da dare ne wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish su uku suka harbe wani jami'in dan sandan Aljeriya har lahira a wani gidan abinci a yankin na Qasnadinah tare da yin awungaba da bindigarsa.
Tags