An Amince Da Sabon Kundin Tsarin Mulkin Kasar Ivory Coast
Rahotanni daga kasar Ivory Coast sun jiyo hukumar zabe na kasar tana cewa al'ummar kasar sun amince da sabon kundin tsarin kasar bayan zaben raba gardamar da aka gudanar a karshen makon nan inda sama da kashi 93 na masu jefa kuri’a suka amince.
Kafafen watsa labarai sun ce jiyo hukumar zaben tana cewa kashi 42.42 cikin dari na al'ummar kasar ne suka kada kuri'arsu a yayin wannan zaben inda kashi 93.42 cikin dari na wadanda suka kada kuri'ar suka amince da sabon kundin tsarin mulkin.
Sabon kundin tsarin mulkin dai ya kumshi dage iyakar da aka sanya na cewa wajibi ne dan takarar shugaban kasar ya zama bai wuce shekaru 75 a duniya ba da kuma kirkiro da mataimakin shugaban kasa da Majalisar Dattijai a kasar..
‘Yan adawar kasar Ivory Coast din sun kauracewa zaben raba gardamar suna masu zargin cewa za a tabka magudi da kuma zargin cewa shugaba Alassane Ouattara na kokarin tabbatar da ikonsa ne kawai a kasar.