Majalisar Afirka Ta Kudu Ta Goyi Bayan Ficewa Daga Kotun ICC
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13363-majalisar_afirka_ta_kudu_ta_goyi_bayan_ficewa_daga_kotun_icc
Majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudu ta goyi bayan matsayar da gwamnatin kasar ta dauka na ficewa daga kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffuka (ICC) bisa zargin kotun da nuna wariya yayin gudanar da ayyukanta.
(last modified 2018-08-22T11:29:11+00:00 )
Nov 04, 2016 05:51 UTC
  • Majalisar Afirka Ta Kudu Ta Goyi Bayan Ficewa Daga Kotun ICC

Majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudu ta goyi bayan matsayar da gwamnatin kasar ta dauka na ficewa daga kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffuka (ICC) bisa zargin kotun da nuna wariya yayin gudanar da ayyukanta.

Rahotanni daga kasar sun bayyana cewar wannan matsaya tana cikin wata sanarwa ce da kwamitin harkokin waje na majalisar ya fitar a jiya Alhamis inda ya ce majalisar kasar Afirka ta Kudun tana maraba da ficewar da kasar ta yi daga yarjejeniyar Roma wacce ta kafa kotun ta ICC.

Har ila yau shugaban kwamitin harkokin wajen na Majalisar Afirka ta Kudun  Mr Siphosezwe Masango ya shaida wa manema labarai cewa lalle sun goyi bayan ficewa daga kotun don kuwa tun da jimawa ake ganin irin nuna wariya da kotun take nunawa da kuma mummunar mu'amalar da take yi da kasashen Afirka.

A kwanakin baya ne dai kasar Afirka ta Kudun ta biyo sahun kasar Burundi wajen sanar da ficewarta daga kotun ta ICC saboda zargin nuna wariya a kan yadda kotun take gudanar da ayyukanta musamman kan shugabanni da kuma 'yan kasashen Afirka.

Kasar Gambiya ma dai ta sanar da ficewar nata.