Buhari Ya Yaba Wa Sojojin Nijeriya Saboda Kwato Wata 'Yar Chibok
Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya jinjinawa sojojin kasar saboda nasarar da suka samu wajen kwato daya daga cikin 'yan matan Chibok din nan da 'yan Boko Haram suka sace sama da shekaru biyun da suka gabata.
Shugaba Buharin ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya fitar a shafinsa na Twitter inda ya ce na sami labari mai faranta rai na sake kwato daya daga cikin 'yan matanmu na Chibok da sojojin Nijeriya suka yi yana mai bayyana sojojin a matsayin wasu gwaraza na kasa.
Shugaba Buhari ya sake jaddda aniyar gwamnatinsa na kwato sauran 'yan matan Chibok din inda ya ce: Babu wani namiji ko mace ko karamin yaro da za a barci a hannun 'yan Boko Haram. Wannan dai shi ne alkawarinmu, kuma muna da niyyar cika wannan alkawari.
A jiya Asabar ne sojojin Nijeriya suka mika Maryam Ali Maiyanga, 'yar makarantar Chibok din da suka kwato din tare da danta dan watanni 10, ga gwamantin jihar Borno bayan da suka kwato ta a yankin Pulka da ke karamar hukumar Gwoza na jihar Borno.
Kwamandan dakarun runduna ta 7 na sojojin Nijeriyan Manjo janar Lucky Irabor ya ce sun sami yarinyar ce a lokacin da suke binciken wasu maboyar 'yan Boko Haram din a dajin Sambisa a jiya.