Mali: An kashe sojan Majalisar Dinkin Duniya Guda Daya
Harin da aka kai wa dakarun majalisar dinkin duniya ya ci ran daya daga cikinsu.
Radiyon Faransa na kasa da kasa, ya ce; Wasu mahara sun kai akan ayarin dakarun majalisar dinkin duniya tare da kashe daya daga cikinsu.
Majiyar soja ta ce; An kai wa ayarin dakarun na Majalisar dinkin duniya da ake kira da; Minosma, hari ne a tsakiyar kasar ta Mali a garin Douentza.
Ayarin ya fara taka wata nakiya ce a gefen hanya kafin daga baya, mahara su bude musu wuta.
Tun a 2012 ne dai kasar Mali ta fada cikin matsalar tsaro bayan da kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi su ka kwace iko da arewacin kasar.
Majalisar dinkin duniya ta kafa rundunar tabbatar da zaman lafiya a kasar bayan da sojojin Faransa su ka fatattaki 'masu wuce gona da iri a arewacin kasar.