Wasu Mahara Sun kai Farmaki Kan Gidan Kurkuku A Kudancin Kasar Mali
Ministan shari'a a kasar Mali ya sanar da cewa: Wasu gungun mahara sun kaddamar da hari kan gidan kurkukun garin Banamba da ke nisan kilomita 100 da birnin Bamako fadar mulkin kasar, inda suka 'yantar da fursunoni 21 da ake tsare da su.
Ministan shari'ar kasar Mali Mamadou Isma'il Konate a yau Litinin ya bayyana cewa: Wasu gungun mahara sun kai farmaki gidan kurkukun garin Banamba da ke gundumar Koulikoro a cikin daren jiya Lahadi, inda suka 'yantar da wasu fursunoni 21 da ake tsare da su.
Mamadou Isma'il ya kara da cewa: Jami'an tsaron gidan kurkuku sun bace babu labarinsu, sai dai har yanzu babu cikakken labarin hakikanin abin da ya faru a yayin kaddamar da harin.
Wasu rahotonni sun bayyana cewa: Gungun maharan sun kuma kai hari kan wani banki a garin na Banamba, inda suka yashe kudaden da suke cikin bankin.
Shaidun ganin ido sun bayyana cewa: Maharan sun tsere ne ta hanyar sahara da ke yankin gabas da kasar Mauritaniya.