An kai hari gidan Yari a Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13567-an_kai_hari_gidan_yari_a_mali
'Yan bindiga sun kai hari kan wani gidan yari a kudancin Mali
(last modified 2018-08-22T06:59:12+00:00 )
Nov 08, 2016 07:40 UTC
  • An kai hari gidan Yari a Mali

'Yan bindiga sun kai hari kan wani gidan yari a kudancin Mali

Wasu 'yan bindiga da ba a gane su ba sun kubutar da firsinoni 21 a garin Banamba da ke kudancin kasar Mali a daren ranar Lahadi,  lamarin da  ministan shari'ar kasar ya kwatanta da "harin ta'addanci".

Mamadou Ismael Konate ya fada a jiya litinin cewa maharan da suka kai hari gidan yari su shine kuma sun je ne  da nufin kwato wasu 'yan ta'adda guda biyu amma  su suka tarar  tuni an mayar da su wani gari.

Ministan ya kara da cewa wani gandiroba ya bace bayan harin da 'yan bindiga suka kai, . Ko da yake ba a san wadanda ke da hannu a harin ba amma a wannan shekara kungiyoyi masu da'awar  kishin addini irinsu Ansar Dine sun tsananta kai hare-hare a cikin kasar ta Mali, inda suka kai hare-hare har guda 60 ciki har da wanda suka kai kan cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da wasu wurare, kana suna kara kutsawa kudancin kasar .