An kama masu zanga-zanga da dama a Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13723-an_kama_masu_zanga_zanga_da_dama_a_masar
Jami'ar tsaron Masar sun cabke masu zanga-zanga da dama a fadin kasar gaba daya
(last modified 2018-08-22T06:59:13+00:00 )
Nov 11, 2016 14:28 UTC
  • An kama masu zanga-zanga da dama a Masar

Jami'ar tsaron Masar sun cabke masu zanga-zanga da dama a fadin kasar gaba daya

A yau juma'a ce Al'ummar kasar Masar suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da hauhawa farashin kayan masarufi a fadin kasar gaba daya, wani jami'in 'yan sandar kasar ya sanar da cewa ya zuwa yanzu kimanin mutane 130 ne daga cikin mahalarta zanga-zangar aka kame, daga cikin su 39 a birnin Alkahira fadar milkin kasar.

Jami'in ya ce 'yan sanda a tsibirin Suez sun tarwatsa wasu tarun mutane da suka taru wuri guda kafin su gudanar da wannan zanga-zanga.

Kungiyoyi masu adawa da Gwamnatin Masar ne suka kira wannan zanga-zanga ta nuna adawa da hauhawa farashin kayan masrufi da kuma siyasar Gwamnatin Abdulfatah Alsese ta hanyar hanyoyin sadarwa na yanar gizo.wacce suka bata lakabi da ranar Tallaka.

Baya ga matsalar tsaro, kasar ta Masar na fuskantar matsalar tattalin arziki, barnar dukiyar Gwamnati, rashin jagoranci na gari, lamarin da ya sanya rashin aikin yi na matasa ya karu da kashi 40%.