Mali: Harin 'Yan ta'adda Akan Barikin Soja
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13813-mali_harin_'yan_ta'adda_akan_barikin_soja
'Yan ta'adda Sun kai hari akan cibiyar soja.
(last modified 2018-08-22T06:59:14+00:00 )
Nov 13, 2016 08:37 UTC
  • Mali: Harin 'Yan ta'adda Akan Barikin Soja

'Yan ta'adda Sun kai hari akan cibiyar soja.

Radiyon Faransa na kasa da kasa, ya ambato majiyar soja na cewa, an kashe sojojin asar biyu da safiyar jiya asabar a wani harin da 'yan ta'adda su ka kai wa sansanin soja a garin Gao.Majiyar sojan ta ci gaba da cewa; An aike da wani ayarin soja zuwa yankin domin korar maharan.

Kungiyar da ta ke kiran kanta 'al-murabidhun' wacce dan ta'addar kasar Aljeriya da aka kashe, Mukhtar Bel Mukhtar, ce ta dauki alhakin kai harin.

Har ila yau, mjiyar sojan ta sanar da cewa; Wasu maharan da ke dauke da makamai sun sace motoci biyu na wani kamfani mai zaman kansa, a arewa maso gabacin gundumar Timbuktu.

Kasar Mali na fuskantar matsalolin tsaro daga kungiyoyin ta'adda.