Somaliya: Sojoji Sun yantar da wani yanki da ke hannun al-shabab.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13957-somaliya_sojoji_sun_yantar_da_wani_yanki_da_ke_hannun_al_shabab.
An kori al-shabab daga wani yanki da ke hannunsu.
(last modified 2018-08-22T06:59:15+00:00 )
Nov 16, 2016 03:32 UTC
  • Somaliya: Sojoji Sun yantar da wani yanki da ke hannun al-shabab.

An kori al-shabab daga wani yanki da ke hannunsu.

Kamfanin Dillacin Labarun Xinhua na kasar Sin, ya ambato wani jami'in soja, na kasar Somaliya, Abdullahi, yana cewa; Sojojin kasar tare da taimakon dakarun Afirka, Amison, sun kwace iko da wani yanki da ke hannun al-shabab.

Kungiyar ta al-shabab ta fice daga yankin da ke kudancin kasar. 

Sojojin kasar ta Somaliya tare da dakarun tabbatar da zaman lafiya na Afirka, suna kokarin tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaben da za a yi a kasar.

Sai dai kungiyar ta al-shabab ta sha alwashin tarwatsa zaben.

A halin yanzu ana gudanar da zaben yan majalisa a duk fadin kasar.