Chadi: An Kame 'Yan adawar Siyasa Da Dama
Nov 18, 2016 19:01 UTC
Jami'an tsaro sun kame 'yan adawar siyasa masu yawa
Radiyon Faransa na kasa da kasa, ya nakalto daga kasar Chadi cewa; A jiya alhamis 'yan hamayyar siyasar kasar sun gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a babban birnin kasar Njamina.
Babbar jam'iyyar hamayyar kasar da ake yi wa lakabi da ( UNDR) ta kirayi 'yayanta da su taru a filin wasa na yanki na 7 a babban birnin, sai dai jami'an tsaro sun yi riga malam masallaci inda su ka hana taron.
Shugaban kasar ta Chadi, Idris Deby Itno ya haramta duk wani taro na 'yan hamayyar siyasa a fadin kasar.
An yi awon gaba da dama daga cikin yan hamayyar.
Tags