Jami'an Sojin Kasar Ethiopia 3 Sun Rasa Rayukansu A Somalia
Nov 20, 2016 05:47 UTC
Sojojin kasar Ethiopia 3 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani bam da aka kai a yammacin jiya a kusa da birnin Kismayo da ke kudancin kasar Somalia.
Shafin labarai na Misri Alyaum ya bayar da rahoton cewa, an kai harin bam din ne a lokacin da sojojin na Habsha da ke cikin rundunar kiyayaye sulhu ta kungiyar tarayyar Afirka suke sintiri a yankin, inda aka halak 3 daga cikin sojojin na Ethiopia.
Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da wannan hari, amma tuni gwamnatin kasar ta Somalia ta dora alhakin hakan a kan kungiyar alshabab, wadda ta saba kai hare-hare makamantan hakan.
Tags