Sojojin Nijeriya Sun Kashe 'Yan Boko Haram Da Dama A Wani Gumurzu
Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya sun bayyana cewar sojojin Nijeriya sun sami nasarar hallaka wani adadi mai yawa na 'yan kungiyar Boko Haram kana wasu da dama kuma sun sami raunuka a wani gumurzu da ya gudana tsakanin bangarori biyun.
Kafar watsa labaran nan ta PREMIUM TIMES da ke watsa labaranta ta internet ta bayyana cewar wata majiya ta shaida mata cewa musayen wutan ya faru ne a lokacin da 'yan Boko Haram din suka kai hari kan wata bataliyan soji ta 119 da ke Kangarwa inda sojojin Nijeriyan suka mayar musu da martani, inda suka sami nasarar hallaka wani adadi mai yawa na maharan da kuma raunata wasu.
Majiyar ta kara da cewa ta kara da cewa wasu sojoji guda 9 sun sami raunuka yayin gumurzun sai dai babu wani da ya rasa ransa.
Wannan dai ba shi karon farko da dakarun Nijeriya suke fuskantar irin wadannan hare-hare daga wajen 'yan Boko Haram din ba. Wasu majiyoyi sun ce wannan shi ne karo na shida da wannan bataliya take fuskantar irin wadannan hare-hare na ba za ta daga Boko Haram din.