Mali : An Kashe Sojoji Biyar A Yayin Zaben Kananan Hukumomi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14218-mali_an_kashe_sojoji_biyar_a_yayin_zaben_kananan_hukumomi
Rahotanni daga Mali na cewa sojojin kasar biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hari da ake kyautata zaton mayakan jihadi ne suka kai masu a lokacin gudanar da zaben kananen hukumomi.
(last modified 2018-08-22T06:59:16+00:00 )
Nov 21, 2016 14:40 UTC
  • Mali : An Kashe Sojoji Biyar A Yayin Zaben Kananan Hukumomi

Rahotanni daga Mali na cewa sojojin kasar biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hari da ake kyautata zaton mayakan jihadi ne suka kai masu a lokacin gudanar da zaben kananen hukumomi.

kamar yadda wata majiyar soji ta shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP ta ce an kai wa sojojin hari ne a yayin ne a yayin da suke kai akwatinan zabe wurin kirga kuri'u a lardin Douentza dake tsakiyar kasar.

Kafin hakan dama an rawaito cewa mayakan jihadin sun kwace kauyen Dilli dake arewacin kasar a kusa da iyaka da kasar Mauritaniya.

Haka Wata majiya tsaro ta kuma shaida cewa maharan basuyi nasara kwace akwatinan zaben, wanda dama nufinsu shi ne lalata tsarin zaben.

Saidai sun  arce da wasu motocin daukan marasa lafiya biyu da kuma motar kantoman yankin, tare da kashe wani fara hula guda.

dama kafin hakan an soke zaben wasu yankuna bakwai dake arewaci wadanda kungiyoyin masu kaifin kishin Islama suka kwace iko lokacin da 'yan tawaye suka yi bore shekaru hudu da suka gabata.