Tunusiya ta hana duban 'yan kasar hadewa da kungiyar IS
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14314-tunusiya_ta_hana_duban_'yan_kasar_hadewa_da_kungiyar_is
Magabatan kasar Tunusiya sun sanar da hana duban matasan kasar hadewa da kungiyar IS
(last modified 2018-08-22T11:29:17+00:00 )
Nov 23, 2016 18:11 UTC
  • Tunusiya ta hana duban 'yan kasar hadewa da kungiyar IS

Magabatan kasar Tunusiya sun sanar da hana duban matasan kasar hadewa da kungiyar IS

Tashar telbijin din Al-Alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta nakalto Hadi Majdub Ministan cikin gida na kasar Tunusiya a gaban 'yan Majalisar Dokokin kasar na cewa daga farkon wannan shekara ta 2016 zuwa yanzu Jami'an tsaron kasar sun samu nasarar dakile bulaguron Matasa sama da dubu 4 zuwa wasu kasashe domin hadewa da kungiyoyi masu hadarin gaske daga cikin su har da kungiyar ta'addancin nan ta IS.

Har ila yau Ministan ya kara da cewa a shekarar da ta gabata bisa hukuncin kotun kasar kimanin mutane 500 ne aka hana fita daga cikin kasar.

Tun bayan harin ta'addancin da Kungiyar IS ta kai wa sansanin Sojojin kasar a  jihar bn Kardan dake kan iyakar kasar da Libiya, Ma'aikatar tsaron kasar ta jibke jami'an tsaro masu yawa domin tunkarar duk wani harin ta'addanci da kungiyoyin 'yan ta'addar ke son kaiwa kasar nan gaba.

A shekarar da ta gabata gumurzu tsakanin Dakarun tsaron Tunusiya da 'yan ta'addar IS ya yi sanadiyar hallaka akala 'yan ta'adda 55 yayin da  Sojojin kasar 12 gami gami da fararen hula 7 suka rasa rayukan su a kan iyakar kasar da Libiya.