Jami'an Tsaron Mali Sun Kame Wani Babban Kwamandan 'Yan Ta'adda A Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14368-jami'an_tsaron_mali_sun_kame_wani_babban_kwamandan_'yan_ta'adda_a_kasar
Majayar tsaron Mali ta sanar da kame wani babban kwamandan 'yan ta'addan kungiyar Ansaruddeen a garin Gao da ke gabashin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:17+00:00 )
Nov 25, 2016 07:06 UTC
  • Jami'an Tsaron Mali Sun Kame Wani Babban Kwamandan 'Yan Ta'adda A Kasar

Majayar tsaron Mali ta sanar da kame wani babban kwamandan 'yan ta'addan kungiyar Ansaruddeen a garin Gao da ke gabashin kasar.

Majiyar tsaron Mali sun bayyana cewa: A wani samame da jami'an tsaron kasar suka gudanar sun yi nasarar kame daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar ta'addanci ta Ansaruddeen kuma shi ne mutum na biyu a cikin jagororin kungiyar a garin Gao da ke gabashin kasar.

Kwamandan 'yan ta'addan na Ansaruddeen yana daga cikin wadanda ake zargi da hannu a kaddamar da harin ta'addanci akn tawagar sojin gwamnatin Mali a makon da ya gabata a garin Tomboukto d ke arewacin kasar lamarin da ya janyo hasarar rayukan sojoji biyar da na wani fafar hula guda.