Jami'an Tsaron Nijar 2 Sun Rasa Rayukansu A Wani Harin Ta'addanci
(last modified Sat, 26 Nov 2016 06:52:22 GMT )
Nov 26, 2016 06:52 UTC
  • Jami'an Tsaron Nijar 2 Sun Rasa Rayukansu A Wani  Harin Ta'addanci

Sojojin Jamhuriyar Nijar biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon wani harin ta'addanci da wasu 'yan bindiga suka kai kansu a kusa da iyakokin kasar da Mali.

Kamfanin dillanicn labaran Xin huwa ya bayar da rahoto daga birnin yamai cewa, jami'an gwamnatin Nijar sun tabbatar da mutuwar sojojin kasar biyu, biyo bayan wani harin kwanton bauna bauna da wasu 'yan bindiga suka kai kan jami'an sojin a yankin Bankilare da ke kan iyakar kasar da Mali, amma babu wani bayani dangane da kungiyar da ke da alhakin kaddamar da harin.

Jamhuriyar Nijar dai na daga cikin kasashen yammacin nahiyar Afirka da suka aike da dakarunsu zuwa kasar Mali karkashin inuwar majalisar dinkin duniya domin gudanar da ayyukan wanzan da sulhu da zaman lafiya a kasar ta Mali, a lokutan baya ma mayakan 'yan tawaye masu tsatsauran ra'ayi a Mali, sun kaddamar da hare-hare makamantan hakan a kan dakarun Nijar da ke cikin kasar ta Mali, da nufin matsa lamba a kan Nijar domin ta janye dakarunta daga kasar ta Mali.