An Gudanar Da Zanga-Zangar Rashin Amincewa Da MDD A Kasar Burundi
(last modified Sun, 27 Nov 2016 05:49:12 GMT )
Nov 27, 2016 05:49 UTC
  • An Gudanar Da Zanga-Zangar Rashin Amincewa Da MDD A Kasar Burundi

Dubun dubatan mutanen kasar Burundi ne suka gudanar da wata zanga-zanga a birnin Bujumbura, babban birnin kasar don nuna rashin amincewarsu da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya da kuma tsoma bakin kasar Belgium cikin harkokin cikin gidan kasar.

Kafar watsa labaran Africanews ya bayyana cewar a jiya Asabar ce dubun dubatan mutanen suka taru a gaban ofishin jakadancin kasar Belgium da ke garin na Bujumbura don nuna rashin jin dadinsu dangane da kafa wani kwamitin bincike da hukumar kare hakkokin bil'adama na MDD yayi bugu da kari kan kan yadda kasar Belgium ta bari wasu 'yan adawan kasar suka halarci wani zama da aka yi a majalisar kasar.

Tun dai bayan fitar da wani rahoto da kwararrun suka fitar dangane da yadda ake take hakkokin bil'adma a kasar Burundin, kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniyan ya fitar da wani kuduri da ya bukata a kafa wani kwamitin bincike na musamman don binciko hakikanin abin da ke gudana.

Masu zanga-zangar dai suna zargin MDD da nuna wariya kamar yadda suka zargi gwamnatin Belgium din da haifar da rikicin siyasa da ke faruwa a kasar sakamakon goyon bayan da take ba wa 'yan adawa da masu haifar da fitina a kasar.