An Tsaurara Matakan Tsaro A Kasar Mali Shekara Guda Bayan Harin Hotel
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14455-an_tsaurara_matakan_tsaro_a_kasar_mali_shekara_guda_bayan_harin_hotel
An tsaurara matakan tsaro a birnin Bamako, babban birnin kasar Mali, a daidai lokacin da ake tunawa da zagayowar shekara guda harin ta'addancin da aka kai hotel din Radison Blu lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 20.
(last modified 2018-08-22T06:59:18+00:00 )
Nov 27, 2016 02:24 UTC
  • An Tsaurara Matakan Tsaro A Kasar Mali Shekara Guda Bayan Harin Hotel

An tsaurara matakan tsaro a birnin Bamako, babban birnin kasar Mali, a daidai lokacin da ake tunawa da zagayowar shekara guda harin ta'addancin da aka kai hotel din Radison Blu lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 20.

Rahotannin sun ce mahukunta a kasar Malin sun karfafa matakan tsaro da sanya shinguna da buhunhuna cike da yashi a helkwatar Majalisar Dinkin DUniy da ke kasar bugu da kari kan sauran gine-ginen gwamnati da sauran wajaje masu muhimmanci.

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta ce a halin yanzu dai an kara karfafa yanayin tsaro a kasar, sannan kuma na baza jami'an tsaro na soji da 'yan sanda, musamman ma a kewayen hotel din.

A ranar 20 ga watan Nuwamban bara ne dai 'yan kungiyar Ansar Dine ta buzaye da suke da alaka da kungiyar Al-Qaid a yankin Maghreb (AQIM) suka kai hari hotel din Radison Blu din da ke birnin Bamako inda suka yi garkuwa da sama da mutane 120, inda daga karshe dai wasu ashirin daga cikinsu suka rasa rayukansu.