Shugaba Zuma Ya Sha Daga Kokarin Tsige Shi Daga Karagar Mulki
Rahotanni daga kasar Afirka ta Kudu sun bayyana cewar shugaban kasar Jacob Zuma ya tsallake wani kokari na tilasta masa yin murabus daga karagar mulkin kasar bayan da uwar jam'iyyarsu ta African National Congress (ANC) ta sake nuna goyon bayanta gare shi biyo bayan kiran da wasu 'yan jam'iyyar suka yi masa na yayi murabus.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce a wata sanarwa da jam'iyyar ANC mai mulkin ta fitar a yau ta ce Kwamitin Zartarwa na jam'iyyar ya goyi bayan shugaba Zuman na ya ci gaba da mulkin kasar bayan da wasu ministoci guda hudu na gwamnatin na sa suka bukaci da yayi murabus daga mukaminsa.
Rahotanni sun ce kira kusoshin jam'iyyar sun gudanar da wani zama a jiya Litinin don tattauna bukatar da wasu ministocin gwamnatin ta Zuma da suka hada da ministan lafiya Aaron Motsoaledi da na ayyuka Thulas Nxesi suka gabatar na cewa wajibi ne shugaba Zuman ya sauka daga karagar mulki, inda bayan tattaunawa mai tsananin gaske 'yan kwamitin zartarwar suka sake bayyanar da goyon bayansu ga shugaba Zuman.
Shugaba Zuman wanda a halin yanzu yake kasar Cuba don halartar jana'izar tsohon shugaban kasar Fidel Castro yana fuskantar suka ne sakamakon wasu batutuwa da ake zarginsa da shi da suka hada da rashawa da cin hanci da kuma gazawa wajen kyatatta tattalin arzikin kasar.