Moroko ta soki aikin Shugabar kwamitin kungiyar Tarayyar Afirka
(last modified Thu, 01 Dec 2016 11:47:21 GMT )
Dec 01, 2016 11:47 UTC
  • Moroko ta soki aikin Shugabar kwamitin kungiyar Tarayyar Afirka

Ma'aikatar harakokin wajen Moroko ta soki Shugabar kwamitin kungiyar Tarayyar Afirka

A cikin wata sanarwa da ta fitar Ma'aikatar harakokin wajen Moroko ta yi suka dangane da aiyukan Nkosazana Dlamini-Zuma a matsayin Shugabar Kwamitin kungiyar tarayyar Afirka, inda sanarwar ta ce Shugabar ba ta yin la'akari na rashin shiga wani bangare a kudirin da take dauka.

Ma'aikatar harakokin wajen Moroko ta zarki Nkosazana Dlamini-Zuma ne da rashin mutunta doka da kuma zartar da dokokin kwamitin Afirka ga kasashe gungu na kungiyar bayan da Shugabar kwamitin ta tarayyar Afirka ta bayyana cewa kokarin da kasar Marokko ke yi na komawa cikin kungiyar Tarayyar Afirka ba zai yi tasiri ba.

A cikin watan Satumbar wannan shekara ne kasar Moroko ta bukaci hadewa da kungiyar Tarayyar Afirkan a hukunce.Shekaru 32 kenan da kasar Marakkon ta fice daga kungiyar Tarayyar Afirkan bayyana adawar ta da bukatar hadawar kasashen yankin yammacin Sahara da ake kira da Westerm Sahara  da kungiyar tarayyar Afirkan.