An fara gudanar da zaben Shugaban kasa a Gambia
Al'ummar kasar Gambia sun fara kada kuri'in zaben Shugaban kasa a fadin kasar baki daya.
A safiyar yau Alkhamis ne ‘Yan kasar Gambia suka fara gudanar da zaben shugaban kasa wanda shugaba mia ci Yahya Jammeh ke neman wa’adin shugabanci karo na biyar bayan shafe shekaru 22 kan karagar mulki.
An bude runfunar zabe da misalin karfe 8 na safe agogon GMT, sannan za a kammala kada kuri’a da misalign karfe biyar na yamma.
‘Yan takara uku ne za suke fafatawa a zaben, da suka hada da Shugaba mai ci Yahya Jammeh da Adama Barrow dan takarar hadakar gungun jam’iyun adawa da kuma Mama Kandeh, wani tsohon dan majalisar dokokin jam’iya mai mulki, da ya tsaya a karkashin tutar wata sabuwar jam’iyya ta GDC.
Sai dai a wannan karon shugaban na fuskantar babban kalubale daga dan takarar hadin gwuiwar ‘Yan adawa Adama Barrow wanda ya sha alwashin kawo karshen shugabancin sheharu 22 na Yahaya Jammeh.
A ranar Talatar da ta gabata, Al'ummar kasar Gambia sun gudanar da gagarumar zanga-zanga ne neman shugaba Jammeh ya sauka daga kan karagar milki.