An fara sanar da sakamakon zaben shugaba kasa a Gambia
(last modified Fri, 02 Dec 2016 11:21:01 GMT )
Dec 02, 2016 11:21 UTC
  • An fara sanar da sakamakon zaben shugaba kasa a Gambia

Sakamakon farko na zaben shugaban kasa a Gambia na nuni da cewa Dan takarar gamayar jam'iyun adawa ne ke kan gaba.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa sakamakon farko da Hukumar zaben kasar ta sanar a wannan juma'a na nuni da cewa Dan takarar gamayar jam'iyun adawa Adama Barrow shi ne ya samu kashi 50% na kuri'un  Banjul baban birnin kasar da aka kidaya, yayin da Shugaban kasar mai barin gado Yahaya Jameh ya samu kashi 43 %.shi kuma Mama Kandeh na Jam'iyar GDC ya samu kashi 7/6 cikin dari.

Ya zuwa yanzu Hukumar zaben kasar ta ce kashi 15% na kuri'un da aka kada ne kawai aka gidaya kuma aka sanar, a yayin ake sanar da wannan sakamakon zabe an karfafa matakan tsaro a birnin na Banjul.

A jiya Alkhamis ne aka gudanar da zaben shugaban kasa a Gambia, inda shugaba Jameh ke kokarin yin tazarta a wa'adi na biyar.