An Kashe Fararen Hula 12 A Gabashin D/Congo
'Yan Tawayen Uganda sun kashe fararen hula 12 a Gabashin D/Congo
Kamfanin dillancin Labaran Reuteus daga birnin Kinshasa ya nakato shugabanin yankin a yau na cewa 'Kungiyar 'yan tawaye da aka sani da "united Democratic Forces» daga cikin kungiyoyin 'yan tawayen kasar Uganda sun hallaka fararen hula a kauyen Mamabiyu mai nisan kilomita 50 daga arewacin yankin Beni dake jihar Kivo ta arewa a gabashin D/Congo. har ila yau 'yan tawayen sun sace kayan dake cikin cibiyar kiyon lafiyan kauyen.
Cibiyar bincike na tabbatar da sulhu, tafarkin Democradiya gami da hakin bil-adama da yaunin tattara bayanai kan cin zarafi da kisan kilan da ake yiwa fararen hula a kasar ta tabbatar da wannan Labari.
Daga watan Oktoban shekarar 2014 zuwa yanzu dariruwan fararen hula ne suka rasarayukansu a kauyukan dake kusa da garin Beni na Kivo na arewa sanadiyar hare-haren da 'yan tawayen Uganda ke kaiwa.
A 'yan kwanakin da suka gabata Dakarun tsaron Beni sun kame wasu Maza biyu da mata guda kan zarkinsu da tusawa matasa ra'ayin cikin kungiyar 'yan tawayen na "united Democratic Forces.