Kananen Yara da dama ke gudun hijra daga Sudan ta kudu.
(last modified Mon, 05 Dec 2016 11:48:04 GMT )
Dec 05, 2016 11:48 UTC
  • Kananen Yara da dama ke gudun hijra daga Sudan ta kudu.

Rikicin Sudan ta kudu ya yi sanadiyar hijrar Duban kananen yarar sudan ta kudu zuwa kasar Uganda

Bisa wani sabon rahoto da babban kwamishinan dake kula da 'yan gudun hijra na MDD ya fitar daga farkon watan yuni zuwa yanzu sama da 'yan kasar Sudan ta kudu dubu 300 ne suka nemi mafaka a kasar Uganda, kuma kashi 60% nada shekaru kasa da 18 sannan sama da dubu 90 'yan kasa da shekaru 7 ne.

Idan ba a manta ba dai, fada ya barke tsakanin Sojojin Gwamnati masu biyayya da Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva keir da kuma masu biyayya da mataimakinsa  Riek Machar a shekarar 2013, lamarin da ya sanya mataimakin shugaban kasar Riek Machar ya yi gudun hijra, bayan kwashe kimanin shekaru biyu ana kwabza fada daga bisani an cimma matsaya na tsagaita wuta kafin daga bisani wani sabon rikicin ya sake barkewa tsakanin bangarorin biyu a cikin watanin da suka gabata.

Fargaba da tsoro ya kara shiga cikin zukatan Al'ummar kasar tun bayan da madugun 'yan tawaye Riek Machar ya shelanta yaki da Gwamnatin kasar.